Rundunar sojan Najeriya ta ce kaida ya canza a yaki da Boko Haram, saboda haka dole ma rawa ta canza. Ma’ana, kodayake da yaki a kasa aka san sojojin kasa, ganin yadda al’amura ke kasancewa an kirkiro wani dan sashin sojojin kasa da za su rika amfani da jiragen sama musamman ma jirage masu saukar ungulu.
Bugu da kari sojojin na kasa sun bullo da wani tsari na hada kai da sojojin sama saboda a gudu tare a tsira tare. Da ya ke jawabi madadin Shugagan Najeriya Muhammadu Buhari a wurin taron sojojin kasa na wannan shekarar da aka yi a Runduna Ta Biyu da ke Ibandan, Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya Laftana-Janar Gabriel Olonisakin, ya ce Shugaba Buhari ya yaba da rawar da sojojin Najeriya ke takawa wajen tabbatar da tsaro a Najeriya.
Mai magana da yawun Rundunar sojojin kasa na Najeriya Birgediya Sani Usman Kukasheka ya tabbatar da bayanin na Janar Olonisakin, sannan ya kara da cewa tuni ma aka bayar da takardar shaidar iya tuka jiragen sama ma wasu sojojin kasa.
Haka zalika sojojin sama na Najeriya su ma sun yi nasu taron a babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja, inda sun ka jaddada shirin aiki tare da sojojin kasa saboda a samu damar murkushe mayakan Boko Haram.
A halin da ake ciki kuma, Kwamandan rundunar yaki da Boko Haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo-Janar Rogers Nicolus ya kama aiki tare da yin kira ga duk wadanda abin ya shafa da a haka kai don tabbatar da zaman lafiya. Ya ce hatta ‘yan Boko Haram ya na kiransu da su fice daga daji su dawo cikin al’umma a gina kasa tare.
Ga dai wakilanmu:
- Hassan Umar Tambuwal da
- Hassan Maina Kaina da
- Haruna Dauda
da cikakken rahoton:
Facebook Forum