Aikin Shedan Ne - Inji Matashin Da Ya Yi Wa 'Yar Shekaru 14 Fyade

Wani matashi mai suna Ishaka Mustapha, dan shekaru 29, da haihuwa da aka kama da aikata laifin yiwa wata yarinya mai shekaru 14, dake tallar Lemu fyde ya ce shedanne ya sa shi aikata wannan danyen aiki.

Matashin mai sana’ar tukin mota ya aikata laifinne ranar 6, ga watan Janairu a wata unguwada ake kira Aremo a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Yarinyar tana tallar lemu ne a unguwar yayin da ustapha ya kirata, kasancewar sabo da tayi da matashin da kuma matarsa, bata yi gaddamar kai masa lemun har cikin dakinsa ba, yayinda shi kuma ya tura matarsa ta je ta debo masa ruwan wanka ba tare da yarinyar ta sani ba.

Da take hira da mujallar Tribune, matashiyar ta bayyana cewa ta yi iyakacin kokarinta, tare da daga murya domin neman taimako amma babu wanda ya kai mata dauki. Ta kara da cewa na fada wa mahafiyata bayan ta dawo saboda jinin yaki tsayawa, inda suka garzaya ofishin ‘yan sanda.

Yayinda ake bincikensa a ofishin jami’an ‘yan sanda ya bayyana cewa matarsa ta tafi dibo masa ruwan wanka lokacida mai tallar ta tambaye shi ya bata ruwan sha, daga nan tace ta gaji dan haka zata zauna ta dan huta, amma ya fada mata cewa zai koma wurin aiki.

Mustapha ya ce “a dai dai lokacinne kawai sai wani abu ya shige ni, nasa kafa ta na shure ta a gaba, sa’annan na yi mata fyade, dana gane cewar ba’a taba amfani da it aba kuma naga tana zubar da jinni, na tuba ga Allah, kuma na nemi gafara daga gareta”.

Bayan kwanaki biyu ‘yan sanda suka yi awon gaba da Mustapha zuwa ofishinsu wajan amsa tambayoyi.

Mai magan da yawun jami’an ‘yan sandan jihar Adekunle Ajisebutu, ya yi kira ga daukacin iyaye da su guji dorawa ‘ya’yansu mata talla ganin irin hadarurrukan da suke fuskanta.