WASHINGTON D C —
Kamar yadda kowane harshe ko kabila ke samun wasu sababbin kalmomi da ke tafiya da zamani, wasu kalmomi kuma ke neman bacewa sakamakon rashin amfani da su, haka matasa a wurare daban daban ke kirkiro wasu bakin kalmomi ko salon mgana domin zantawa da juna ba tare da wasu baki sun fahimci sakon da suke aikawa juna a lokacin ba.
Ta dalilin haka ne muka sami zantawa da wani matashi mai suna Ibrahim Abdullahi, wanda ya bayyana cewa a duk lokacin da kaji matasa a yankinsu sun ambaci “kidan janaral a sama” suna nufin gari yayi zafi Kenan.
Ya take a yankinku, wane salon Magana matasa ke amfani da ita data yi dai dai da zmani?
Saurari wasu bakin kalamai adaga Ibrahim Abdullahi a nan.