Babban abin da ya fi ci mana tuwo a kwarya shine yadda al’umma ke kin karbar sabon abu da ya shigo masu musammam ma a faggen waka inji Buzo Dan Fillo .
Sadik Salihu Abubakar, ya kara da cewa har ila yau akwai kalubale wajen gudanar da ayyukansu ta amfani da na’urarorin kamputa ko Kyammarar daukar hoto wanda a mafi yawancin lokuta, ba’a samun matasa ‘yan arewa wadanda suka iya amfanin da wasu na’urorin ko suke da kayan aiki na zamani har sai sun dangana da wasu garuruwa kamar su Kaduna, ko Jos, wata rana ma har zuwa Lagos.
Ya ce baya ga waka da ya ke yi, yakan ziyarci wasu wuraren da ake shirya fina-finan kasashen waje da wasu harsuna kuma yakan fassara su zuwa harshen Hausa domin saukakawa masu kallo.
Buzo Dan fillo, ya bayyana cewa waka wata hanya ce da ake aikawa al’umma sako cikin suri, haka kuma ana amfani da ita wajan koyawa yara karatu da sauransu, kai hatta kamfanoni kan amfani da waka wajan tallata kayayyakinsu.