Ahmad Musa: Ya Kamata Abi Kadin Kwallayen Da Aka Zura

Dan wasan kwallon kafa na Super Eagles a tarayyan Najeriya, Ahmed Musa ya bukaci Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika da ta kaddamar da bincike, domin tantance sahihancin kwallaye 2 da Super Eagels ta jefa a ragar Afrika ta Kudu.

Amma alkalin wasa mai suna Bakary Gassama ya haramta cin a karawar da suka yi na wasan neman cancatar shiga gasar cin kofin na Nahiyar Afrika na 2019.

Alkalin wasan dan asalin Gambia, Bakary Gassama ya soke kwallayen da dan wasan gaba na Najeriya Kelechi Iheanacho da Ahmed Musa, suka zura a ragar Afrika ta Kudu ranar Asabar da ta gabata.

Sai dai tuni alkalin ya amince da tafka kuskure kan lamarin, sannan kuma ya nemi afuwa daga wajan Ahmed Musa, in da ya bayyana cewa haka abun yake, domin wataran lokaci zuwa lokaci ana samun irin wadannan kuskuren,
musamman saboda rashin na’urar mai taimakawa alkalin wasa (VAR).

Ku Duba Wannan Ma Dan Wasa Kevin De Bruyne Zai Koma Fagen Taka Leda

Duk da kashe wannan kwallaye biyu da akayi wa Najeriya ta samu nasarar samun tikitin halartar gasar cin Kofin Afrika a Kamaru a shekara mai zuwa inda aka tashi wasan 1-1 da akayi a Afrika ta Kudu a Johannesburg.

Najeriya tana da maki goma ne a teburin sai Bafana Bafana ta Afrika ta kudu take biye da ita a mataki na biyu da maki tara.

Najeriya zata buga wasanta na karshe da kasar Seychelles a Najeriya, sai kuma Libya ta karbi bakuncin Afrika ta Kudu, a wasansu na karshe a rukunin (E).