A shirye shiryenta domin fafatawa a wasan neman cancatar shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka a shekarar 2019, tsakanin Najeriya da Kasar Afrika ta Kudu a karshen mako mai zuwa a can Johannesburg.
Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles dake tarayyan Najeriya zata shiga sansanin horas da 'yanwasa inda ake sa tsamanin isowar babban mai horas da tawagar ta Super Eagles Gernot Rohr filin bada horan dake Asaba jihar Delta a yau Litinin.
A wata hira da yayi da manema labarai Jami'in watsa labarai na Kungiyar Mr Toyin Ibitoye, yace hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya ta (NFF) ta kammala duk wani shirye shirye da ya kamata na isowar 'yanwasan da aka gayyata a sansanin na filin wasan tunawa da Stephen Keshi dake Asaba, inda zasu fara karban horo tun daga ranar Talala, kafin daga bisani su tashi zuwa kasar Afrika ta Kudu, ranar Alhamis ko kuma Jumma'a.
Haka zalika ya kara da cewar kan lafiyar 'yanwasa babu dan wasa daya da yake da wani rauni a cikin wadanda aka gayyata, kuma likitan Kungiyar zai cigaba da duba lafiyar 'yan wasan domin tabbatar da isashiyar lafiyarsu kafin wasan.
Wannan wasa shine karawarsu ta biyu a matakin rukuni inda a haduwarsu na farko kasar Afrika ta Kudu ta doke Najeriya daci 2-0 a Uyo jihar Akwa Ibon dake Najeriya.
A rukunin Najeriya ce take saman teburin wannan wasan da za'ayi, shine zai tabbatar da cewa ta samu tabbacin tikitin gasar ta Nahiyar Afrika in har ta doke Bafana Bafana, ko kuma tayi canjaros.
Facebook Forum