Kamfani sadarwar Najeriya na Main One ya dauki alhakin wata 'yar tangarda da ta yi sanadiyar bida hanyoyin yanar gizo da sadarwar kamfanin Google ta China da Rahsa na wani dan lokaci, kamfanin na mai cewa akan kuskure ya haddasa matsalar a lokacin da yayi wani garambawul akan hanyoyinsa, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.
Batun ya bayyana ne ranar Litinin da rana,a yayin da kamfanonin ThousandEyes da BGPmon masu sa ido akan yanar gizo suka ce an bida hanyoyin da sakonnin yanar gozon kamfani Alphabet na Google ta China da Rasha, abinda ya janyo damuwa akan cewa da gangan aka yi kutse a hanyoyin bayanai da na sadarwar yanar gizon.
A wani sako da kamfanin na Main One ya tura ta hanyar email, ya ce abinda ya faru ya kawo tangardar daukewa hanyar sadarwa har na tsawon minti 74, Wannan dalilin ne ya sa aka bi da hanyar sadarwar kamfanin Google ta takwaran kamfanin sadarwar Main One dake China, a cewar kamfanin dake Yammacin Afrika.
Kamfanin Google bai yi bayani sosai ba akan matsalar. Ranar litinin kamfani dai ya yarda cewa sun fuskanci matsala a wani sako da ya tura ta shafinsa na yanar gizo wanda ya ce ana bincike akan matsalar da aka samu kuma yana kyautata zato matsalar ta fara ne daga wajen kamfanin.
Kamfanin na Google dai bai fadi yawan mutanen da matsalar ta shafa ba ko ya iya gano wadanda abin ya shafa.
Facebook Forum