Kungiyoyin kwallon kafa na firimiya lig dake kasar Ingila zasu fara sanya 'yanwasan ketare 12 cikin 25 na tawagar 'yanwasan su, karkashin shirye shiryen sabon tsari na hukumar kwallon kafa ta kasar (FA).
Dan wasan baya na kasar Brazil mai taka leda a Kungiyar kwallon kafa ta Paris-saints German, Dani Alve mai shekaru 35, da haihuwa yace yana da sha'awar buga wasa a bangaren gasar firimiya lig na lngila kafin yayi murabus daga wasan kwallon kafa.
Borussia Dortmund da Marseilles sun jera sahu guda wajan zawarcin matashin danwasan tsakiya na Kungiyar Arsenal mai suna Ben Cottrell, dan shekaru 17 da haihuwa dan kasar Ingila.
Dan wasan tsakiya na Tottenham Mousa Dembele ya sauka a kasar Qatar domin karban jinya na raunin da yayi a idon sawunsa, dan wasan dan kasar Belgium ya samu rauni ne a wasan da suka doke kungiyar Wolves daci 3-2, inda bayan anyi bincike aka fahimci cewar ya samu matsala da jijiyoyinsa.
Kungiyar kwallon kafa ta Brighton, tace ba zata daukaka wani kara ba a kan Jan Katin da danwasanta Dale Stephens ya samu a wasan da sukayi da Cardiff City ranar Asabar inda aka tashi 2-1.
Tun a kimanin mintuna 34 aka bashi Jan Kati sakamakon wani laifi da yayi, wanda hakan yake nuni da cewar dan wasan ba zai buga wasanni uku a Jere ba nan gaba.
Facebook Forum