Taron wanda ke samun halartar wasu daga cikin shugabanin kasashe irinsu Mohamed Bazoum na jamhuriyar Nijer lokaci ne na tattauna hanyoyin karfafa harakokin kasuwanci da zuba hannun jari don bunkasa kamfanoni da masana’antu a nahiyar Afrika.
A yayin wannan haduwa ta tsawon kwanaki 4, za a saurari bahasi daga mutane 100 da suka hada da shugabanin kamfanoni da ministoci dangane da sabbin hanyoyin kasuwanci da na zuba hannun jari da irin alkawuran da ake ganin za su ba da damar karfafa harakoki a tsakanin Amurka da kasashen Afrika ta yadda nahiyar za ta amfana da wannan hulda fiye da yadda abin yake a baya.
Tsohon dan majalissar dokokin kasa Abdoul Moumouni Gousmane na ganin yiwuwar Afrika za ta ci gajiyar shirin ta hanyar abin da ke zama sabon samfari.
Akalla mutane 1000 ne ke halartar zaman taron na wannan karo. Shugaba Mohamed Bazoum na Nijer na daga cikin shugabanin kasashen da aka gayyata a matsayin bakin musamman a wannan taro, sai wasu ministoci daga kasashe 25 na Afrika, da kuma tawwagar wasu jami’an gwamnatin Amurka su 50.
Masanin tattalin arziki Dr Soly Abdoulaye na ganin wannan a matsayin wata damar da shugabanin nahiyar za su yi magana da baki guda domin morar arzikin da Allah ya baiwa nahiyar.
Amurka da Afrika na da dadaddiyar huldar kasuwanci a karkashin tsarin da ake kira AGOA, to sai dai an dan fuskanci cikas a shekarun baya saboda dalilan siyasa , mafari kenan da ya sa wasu ke daukar taron a matsayin hanyar warware bakin zaren.
A shekarar 1997 ne gwamnatin Amurka ta fara shirya wannan taro da aka damka al’amuran tsare-tsarensa a hannun sashen hulda na Corporate Council on Africa CCA, kuma wannan shine karo na 5 da wata kasar Afrika ke karbar bakuncinsa.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5