Wasu 'Yan Kasashen Larabawa Suna Zanga Zanga Ta Kona Kansu

Dan kasar Masar Mai gidan cin abinci,Abdouh Abdel Moneim,dan shekara 48 da ahifuwa a gadon asibiti,bayan ya kona kansa a harabar majalisar dokokin kasar.

Masu zanga a Masar,da Mauritania da Aljeriya sun bankawa kansu wuta,a wani lamari da ake gani tamkar kwaikwayon abinda ya janyo tarzomar siyasar da ta afkawa kasar Tunisia.

Masu zanga a Masar,da Mauritania da Aljeriya sun bankawa kansu wuta,a wani lamari da ake gani tamkar kwaikwayon abinda ya janyo tarzomar siyasar da ta afkawa kasar Tunisia.

Jami’an Masar sunce an kwantarda Abdou Abdel Moneim Hamada,dan shekaru 48 da haifuwa,mai gidan cin abinci,bayan ya bankwa kansa wuta a harabar majalisar dokokin kasar a Alkahira.

A kasar Mauritania kuma,Yacoub Ould Dahoud, ya bankawa kansa wuta cikin wata mota da yake ciki a kofar fadar shugaban kasa. Shi ma an kai shi asibiti.

Duka mutanen biyu an bayyana cewa suna bayyana rashin gamsuwa da yadda gwamnatocin kasashen suka tafiyar da al’amuran jama’a.

Amma a Aljeriya mutane hudu ne suka kona kansu cikin makon jiya.

Da alamaun wadan mutanen suna kwa-kwayon wani dan kasuwa a Tunisia da ya kashe kansa ta kona kansa saboda hukumomi sun kwace kayan hajarsa. Lamairin ne ya haifar da zanga zangar da ta kai ga tilastawa shugaban kasar Ben Ali barin kasar.