Shugaban rikon kwarya na kasar Tunisiya ya kafa gwamnatin hadin guiwa yau lahadi, bayan hambare gwamnatin tsohon shugaban kasar Zine El Abidine Ben Ali wanda ya yi mulki na tsawon shekaru ishirin da uku. An rantsar da kakakin majalisar dokokin kasar Foud Mebazza a matsayin shugaban kasa na wucin gadi jiya asabar, kwana daya bayanda shugaba Ben Ali ya tsere zuwa kasar Saudiya. Mr. Mebazza yace ya umarci PM kasar ya kafa gwamnatin hadin guiwa. Majalisar tsarin mulkin kasar ta umarci a gudanar da zaben shugaban kasa cikin kwanaki sittin. An ji karar bindiga jiya asabar yayinda ‘yan sanda da tankunan sojoji suke sintiri bisa titunan da har yanzu suke sike da tarin shara sakamakon tarzomar da kwasar ganima da aka shafe dare ana yi. Sai dai babu wata alamar barkewar wani sabon tashin hankali yau lahadi.
Shugaban kasa na rikon kwarya a Tunisiya ya kafa gwamnatin hadin guiwa.