Misali a lokacin Shugaba Barack Obama mai barin gado aka bude wani sabon babin huldar diflomasiya da kasashen Afirka.
Amma a ra'ayin Mamman Sani Adamu mai sharhi akan alamuran yau da kullum nahiyar Afirka ba kashin yarwa ba ce ga kasashen yammacin turai da Amurka kanta.
Misali yace Afirka ita ce take bada kashi 25 cikin 100 na bukatun man fetur din Amurka. Kana Afirka tanada dimbin arzikin ma'adanai da Amurka ke bukata.
Saidai babban kalubale shi ne yadda China ke habaka huldar cinikayya da kasashen Afirka wanda ita Amurka zata yi iya kokari tayi zagon kasa.
Juyawar harkokin mulki daga hannun Democrat zuwa Republican wani abu ne da Alkasim Abdulrahaman ke kallon ya fi wa kasashen Afirka alfanu saboda lura da wasu abubuwa can baya.
Yace duk lokacin da Republican suke mulki Afirka ta fi cin moriyar mulkin da alaka da Afirka. Amma duk lokacin da Democrat suke kan mulki taimakon da ake samu yana raguwa. Saboda haka Alkasim yace suna kyautata tsammanin Afirka zata ci moriya kamar lokacin Reagan da su Bush.
Amma kasancewa Donald Trump mutum ne mai fadin abun da ya ga dama ba tare da yin la'akari da ra'ayin wasu ba shugabannin Afirka da na nahiyar Turai zasu yi dari-dari dashi tukun na har sai sun san yadda danganta zata kasance.
Misali da alama Trump na fatan tarayyar Turai zata rushe saboda ya yabawa Birtaniya da ficewa daga kungiyar. Irin wadannan kalaman na Trump zasu kawo rudani. Haka kuma aniyarsa ta yin kunnen shegu da duk wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya zai kawowa kasashe rudani.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5