To sai dai kuma har yanzu cece ku cen da suka dabaibaiye zaben har yanzu suna ci gaba da kanainaiye harkokin siyasar Amirka.
Domin kwa ana ta muhawarar akan bayanin da jami’an leken asirin Amirka suka yi, cewa kasar Rasha tayi shishigi a zaben shugaban kasar Amirka domin Donald Trump ya lashe zabe.
Ya zuwa yanzu kuma, akalla wakilan Majalisar dokokin Amirka guda goma sha takwas, yan jam’iyar Democract ne suka ce ba zasu halarci bikin rantsar da Donald Trump ba.
Ana sa ran cewa kimamin mutane dubu dari takwas zuwa dubu dari tara ne zasu zo nan Washington DC domin su shedi bikin rantsar da Mr. Trump, sai dai kiyasin bai kai yawan wadanda suka shedi bikin ranar rantsar da shugaba Barack Obama ba
Kuma akwai mutane da dama da zasu zo domin yin zanga zangar nuna rashin amincewa.
A wata hirar hadin gwiwa da jaridar The Times of London da kuma jaridar Bild ta kasar Jamus suka yi da shugaba mai jiran gadon Donald Trump, yayi abinda ya saba yi
Yace yana mutunta shugabar Jamus Angela Merkel. To amma ta yi mumunan kuskure data bari dubban yan gudun hijira suka shiga Jamus.
Yawancin yan gudun hijirar Musulmi ne wadanda suka kwarara zuwa turai domin arcewa yaki da ta’adanci da kuma fatara.