A taron da aka gudanar a birnin Addis Ababa, ya nuna yadda kawunan kasashen ya hade game da matakin shugaban Amurka na hana wasu kasashen Afirka shiga Amurka.
Matakin hana kasashen musulmi bakwai izinin shiga Amurka bai zo da mamaki ba, kasancewar tun da tun lokacin kamfen shugaba Trump ya yi alwashin hana al’ummar irin wadannan kasashen izinin don a ganin itace hanyar kawar da aikin ta’addanci.
Shugabar sakatariyar AU a Addis Ababa Nkosazana Dlamini Zuma, tace Afirka na fuskantar wata guguwar diplomasiyya, yayin da Amurka ta ci gajiyar baya daga Afirka yanzu ta dauki matakin hana ‘yan gudun hijira daga wasu daga kasashen shiga Amurka.
Kungiyar AU bata ware kasashe kamar su Somalia ba, wadda daman ba ta shiri da Amurka, inda aka ci zarafin gawarwakin wasu Amurkawa da aka kashe a Mogadishu. Ko Sudan da ake zargi da mallakar wata cibiyar makamai da kuma neman da kotun duniya ke yiwa shugaba Al-Bashir ruwa a jallo, da kuma Libiya inda wasu da suka fusata bayan kashe shugaba Mohammad Gaddafi, suka hallaka jakadan Amurka a Benghazi.
Masanin ta’addancin ‘kasa da ‘kasa Dakta Mohammad Bello na jami’ar Dutse, yace AU na yin rigakafi ne da yafi magani don kar daga kasashen uku a sake ambatar wasu kasashen.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5