Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kwastam Ta Kama Wasu Makamai A Legas


Bindigogi
Bindigogi

Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya ta kama wasu makamai masu yawa da aka yi kokarin shigar da su Najeriya.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama wasu akwatuna dauke da bindigogi 661 a cikin wasu akwatuna 49 da ake tafiya da su a wata mota a yankin Apapa dake Legas.

Kakakin hukumar Kwastan mai kula da shiya ta shida Mista Jerry Attah, ya fadawa Muryar Amurka cewa yanzu haka an kama wasu jami’an hukumar biyu da kuma wasu fararen hula biyu.

Sai dai har yanzu ba a bayyana sunayen mutanen da ake zargi da yanzu haka ke hannun hukuma ba. wannan lamari dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumomin tsaro ke kokarin dakile ayyukan ta’addanci da maido da zaman lafiya a Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG