Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Malaman Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha Na Najeriya Sun Shiga Yajin Aiki


Taron Manema Labaru na Kungiyar Malaman Kwalejoji
Taron Manema Labaru na Kungiyar Malaman Kwalejoji

Malaman Kwalejojin kimiyya da fasaha mallakar gwamnatin tarayyar Najeriya da na jihohi sun fara yajin aikin gargadi na tsawon mako guda.

Yajin aikin dai ya fara ne daga missalin karfe 12 na dare a matsayin gargadi, kuma idan har ba a samu daidaito ba zai kasance har sai illa baba ta gani.

Da yake zantawa da manema labarai shugaban kungiyar malamai na kwalejin Tatara Ali Polytechnic, Kwamrad Mohammad Bala Yakubu, ya nemi da daina cin zarafin malamai da katsalandan a harkokin kungiyar malaman da kuma biyan albashin da ya kamata.

A cewar shugaban malaman yanzu haka akwai malaman kwaleji a wasu jihohin Najeriya dake bin bashin al’bashinsu har na tsawon watanni bakwai har zuwa 14. Dokokin kungiyar dai ya bayar da damar tafiya yajin aiki na mako guda, wanda idan har ba a cimma matsaya ba malaman zasu iya tafiya yajin aikin sai baba ta gani.

Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Mohammad, ya zanta da wasu ‘dalibai wanda suka nuna rashin jin dadinsu ga yajin aikin ganin cewa babu abin da zai haifarwa ‘dalibai sai ci baya, sun kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki matakin da ya kamata wajen sasantawa da malaman domin a koma makaranta.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG