Mataimakin shugaban jami'ar ya yi wannan furucin ne lokacin da yake karbar kwamitin da shugaban kasa ya kafa na sake gina arewa maso gabashin Najeriya lokacin da mambobin suka ziyarceshi.
Kwamitin a karkashin jagorancin mataimakin shugabanta ya isa jami'ar ne domin jajanta masu saboda tashin bamabamai da aka samu a jami'ar kwana kwanan nan da suka yi sanadiyar mutuwar mutane har da wani shehu malamin jami'ar.
Farfasa Abubakar Njodi yace yanzu lokaci ne da za'a tashi tsaye domin tabbatar da samun ingantacen ilimi a yankin arewa maso gabas ganin yadda kungiyar Boko Haram tayi katutu a yankin da irin illolin da kungiyar ta jawo musamman a fannin ilimi. Ta'adancin 'yan Boko Haram din ba karamin koma baya ya kawo ba.
Farfasa Njodi yace tun kafin ma a shiga rikicin Boko Haram aka sanarda sakamakon wani binciken da ya nuna arewa na bayan kudu a harkokin ilimi da shekaru dari. 'Yan Boko Haram sun sake dagula ilimi musamman a arewa maso gabashin Najeriya. Koda kudancin Najeriya zata daina karatu yau, arewa gaba daya ba zata cimmata ba sai nan da shekaru dari.
Farfasa Njodi ya kira 'yan arewa su tashi su habaka harkokin ilimi idan har ana son a cigaba.Yace idan aka kasa jihohin arewacin Najeriya kashi-kashi, arewa maso yamma, arewa ta taskiya da arewa maso gabas, za'a ga cewa arewa maso gabas tana koma baya da shekaru dari da hamsin wajen ilimin zamani. Ya kamata a gane cewa harkokin ilimi a wannan yankin ya lalace fiye da abun da ake tsammani saboda haka akwai jan aiki da ya kamata a yi. Dole a soma da wuri-wuri.
Farfasa Abubakar Njodi yace a matsayinsu na kasancewa jami'a dole ne su ilimantar da mutanensu domin cigaban kasar Najeriya. Daga bisani ya godewa gwamnatin Buhari da kafa kwamitin domin sake gina yankin.
Haruna Dauna nada karin bayani.