AFCON 2023: Najeriya Ta Dare Saman Teburin Rukunin A

'Yan wasan Najeriya (Hoto: Twitter Super Eagles)

Rabon da Najeriya ta samu irin wannan garabasar kwallaye tun a shekarar 1959 inda ta lallasa kasar Benin, a lokacin tana amsa sunan Dahomey, inda aka tashi da ci 10-1.

Najeriya ta gyara zamanta a saman teburin wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a rukunin A.

‘Yan wasan Super Eagles sun doke Sao Tome da ci 10-0 a wasan da suka kara a ranar Litinin a wasansu na biyu.

Yanzu suna da maki 6 a rukunin wanda ke dauke da Guinea Bissau, Sao Tome da Saliyo.

A wasanta na farko, Najeriya ta doke Saliyon da ci 2-1 a Abuja a makon da ya gabata.

Rabon da Najeriya ta samu irin wannan garabasar kwallaye tun a shekarar 1959 inda lallasa kasar Benin, a lokacin tana Dahomey, inda aka tashi da ci 10-1.

A badi ne kasar Ivory Coast za ta karbi bakuncin gasar a tsakanin 23 ga watan Yuni zuwa 23 na watan Yuli.

Guinea Bissau ce ke biye da Najeriyar a rukunin na A da maki 4.