Jirgin ruwan ya kife ne a ranar Juma’ar da ta gabata, sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a yankin Ogbaru da ke Anambra, kamar yadda jami’ai suka bayyana a ranar Asabar, inda suka ce akalla mutane 10 ne suka mutu yayin da wasu 60 suka bace.
A wata sanarwa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Twitter jiya Lahadi, ya ce hukumomin gaggawa sun tabbatar da adadin wadanda suka mutu ya karu.
Hukumomin kasar na kokarin ceto duk wani fasinja da ya bata, in ji Buhari, ya kuma umurci hukumomin da abin ya shafa da su duba ka’idoji don hana afkuwar hadurra a nan gaba.
Shugaban Hukumar bada Agajin Gaggawa ta Jihar Anambra ya ce an ceto mutane 15 a daren Asabar.
Anambra na cikin jihohi 29 daga cikin 36 na Najeriya da suka fuskanci ambaliyar ruwa a bana. Ruwan dai ya yi awon gaba da gidaje da amfanin gona da tituna tare da shafar akalla mutane rabin miliyan.