ABUJA: ICPC Ta Kaddamar Da Kungiyoyin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa A Makarantu 30

Wasu dalibai a jihar Legas

Wasu dalibai a jihar Legas

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta Najeriya ICPC, Dr. Musa Adamu Aliyu, SAN, ya bukaci daliban kasar da su tashi tsaye domin daukar nauyinsu a matsayin masu kawo sauyi da Najeriya ke matukar bukata wajen dakatar da cin hanci da rashawa musamman a makarantu.

WASHINGTON, D. C. - Ya yi kira ga ‘yan makarantar a umarnin da ya bayar yau a wajen bikin kaddamar da kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa na dalibai 30 a makarantu 30 da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.

A cikin jawabinsa ga daliban, Dr. Aliyu, ya shaida wa daliban cewa, tun da sun gane wa idanunsu matsalolin cin hanci da rashawa a makarantu tun daga malaman da ke neman cin hanci, lalata da kuma rashin zuwa makaranta, yana da muhimmanci su yi amfani da karfinsu wajen sauya lamarin.

Ya ce “a matsayinku na shugabannin Najeriya na gaba, yana da mahimmanci ku yi amfani da zabinku, muryarku da kuma kudurinku don canza makarantun Najeriya su zama ginshikan gaskiya da nagarta. Kuna iya zama masu fallasa munanan abubuwa, kuma ku kai rahoton ayyukan cin hanci da rashawa ga ICPC. Ta hanyar nuna adawa da ayyukan da ba daidai ba, kun zama wakilai na canji, da rikon amana da gaskiya a cikin makarantunmu,”

Shugaban hukumar ta ICPC ya bayyana cewa,kungiyoyin na da nufin yakar kalubalen cin hanci da rashawa a makarantu musamman ganin cewa, ba su tsira daga kalubalen cin hanci da rashawa da ya dabaibaye azuzuwa ba, da lalata jarabawa da bata sunan tsarin karatun kasa, musamman da badakalar satifiket na bogi da ya girgiza cibiyoyin mu.

A cewarsa, Ta hanyar kafa kulob a makarantu, ICPC tana nufin hada kai don yaki da cin hanci da rashawa tun daga tushe, tun daga shugabanninmu na gaba.