Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci Da Ake Yi Wa Kwamitin Majalisar Wakilai Kan Badakalar Ayyukun Yi


Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci
Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Hukumar, Azuka Ogugua. 

Hukumar ICPC ta ce ta fara bincike kan zargin cin hanci da ake yi wa Kwamitin Majalisar Wakilai kan badakalar ayyukan yi da kuma rashin gudanar da ayyuka a ma'aikatu da hukumomin Gwamnati, amma masani a fannin siyasa da diflomasiyar kasa da kasa, ya ce an dade ana ruwa kasa na shanyewa a harkar bincike a Majalisar Tarrayya.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Hukumar, Azuka Ogugua.

Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci
Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci

Ogugua ya ce Hukumar ICPC ta samu koke ne daga Shugaban Kwamitin wucin gadi na Majalisar Wakilai, Yusuf Adamu Gagdi. Koken na cewa wata kafa ta yanar gizo ta wallafa wani labari da ke cewa wasu mambobin kwamitin sun nemi cin hanci daga wurin Shugabannin Manyan Makarantun Kimiyya da fasaha, da su biya su wasu Kudade a asusun ajiya a matsayin cin hanci.

Amma Shugaban Hukumar Manyan Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Kasa, Dokta Yahaya Umar Bande ya ce babu kamshin gaskiya a wannan labarin.

Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci
Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci

Bande ya ce shi ya yi rantsuwa a gaban kwamitin domin wannan shi ne karon farko da Hukumar ta taba zuwa Majalisar Dokokin Kasa, saboda haka babu yadda za a ce an gana da wasu 'ya'yan kwamitin da ba a san su ba. Bande ya ce Hukumar ba ta sa wasu kudi a asusun kowa ba kuma ba za ta taba yin irin wannan abu da ya jibanci cin hanci da rashawa ba, domin akwai dokoki a kasa wadanda a yanzu za su iya sawa a binciko gaskiyar al'amarin. Bande ya ce in an samu wani jami'in kungiyar da laifi, a hanzarta hukunta shi.

Amma Masanin harkoin Siyasa da Diflomasiyar kasa da kasa kuma Malami a Jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokacin kan batun.

Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci
Hukumar ICPC Ta Fara Binkicen Zargin Cin Hanci

Bibi ya ce ba yau ne aka fara zargin kan bincike da Majalisar Dokoki ke yi ba, wannan ya biyo bayan yunkuri da suke yi kullum, amma ba a gani tasirin bincike da suke yi. Bibi ya ce sai fa Majalisa ta sauya salon binciken ta, inda 'yan kasa za su ga banbanci, wallau a kai ga gurfanar da masu laifi a gaban kuliya ko a hukunta wadanda aka samu da laifi. Bibi ya ce matukar ba a yi haka ba, to, kullum sai an yi masu irin wadannan zargi.

Shi kuwa Shugaban Kwamitin Wucin Gadi na Majalisar Wakilai Yusuf Adamu Gagdi ya ce shi ne ya nemi Hukumar ICPC ta shiga lamarin, ta binciki lambar asusun da aka ruwaito a dandalin sada zumunta din, domin a gano mai shi. Gagdi ya ce kwamitin yana kunshe ne da mutane 37 wanda aka dora wa nauyin binciken ma'aikatu da hukumomin Gwamnati 900, abu ne mai wuya mutum ya yi shaida kan kowa da kowa.

Kwamitin ya kwashi makonni 6 yana gudanar da bincike, kuma har yanzu ya na cigaba da binciken duk da cewa Majalisar Kasa tana hutu a halin yanzu.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG