SOKOTO, NIGERIA -A Najeriya daidai lokacin da guguwar siyasa ke kadawa, masu son tsayawa takara na ci gaba da bayyana anniyar su, sai dai wani abu da ya fara daukar hankalin jama'a shi ne yadda ‘ya'yan wadanda suka saba rike madafun iko ke fitowa neman manyan mukamai.
A dai yanzu cikin kasar a iya cewa hada-hadar neman mukaman siyasa ta kankama musamman a jam'iyun da suka fara sayar da takardun cikawa don neman tsayawa takara.
A wannan karon 'ya'yan tsofaffin gwamnoni sun fra nuna sa'awar tsayawa takara. Daga cikin wadanda suka nuna sha'awar tsayawa takara daga jihar Jigawa akwai Mustapha Sule Lamido ‘dan tsohon gwamna Sule Lamido, a jihar Sakkwato kuma da Sagir Attahiru Bafarawa ‘dan tsohon gwamna Bafarawa da Mahdi Aliyu Gusau ‘da ga tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara akan tsaro suna neman tsayawa takarar kujerar gwamna a Jihohin su.
Ku Duba Wannan Ma Shugaba Buhari Ya Ce Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC Ya Farfado Da KimartaHakan ya sa wasu na kallon lamarin tamkar ana son mayar da kujerar ta gado, sai dai Sagir Attahiru Bafarawa da ya nemi tsayawa takarar a Sakkwato ya ce ba haka abin yake ba.
Masharhanta na ganin cewa ana iya kallon wannan lamarin ta fuskoki da dama kamar fuskar doka da kuma cancanta.Barrister Mu'azu Liman Yabo na cikin masu wannan ra'ayin.
Har yanzu akwai masu son tsayawa takarar kujerar gwamna da dama da suka ki bayyana anniyar su a fili abin da masana ke ta'allakawa da siyasar uban gida, suna jiran amincewar uwayen gidan su, wanda ba zai kai Najeriya ga ci gaban da ‘yan kasa ke muradi ba.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5