Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Wasu Mata Ke Fafutukar Neman A Dama Da Su A Fagen Siyasar Najeriya


Hajiya Maryam Mamman Nasir
Hajiya Maryam Mamman Nasir

Mata a Najeriya sun dade suna neman a dama da su musamman a fannin siyasar kasar.

Ko a kwanakin baya mata sun gudanar da zanga-zanga, inda suka mamaye gaban majalisar dattawan kasar don tabbatar musu da kudurorinsu da suka hada ba su kaso 35 cikin 100 na wakilci a siyasa da majalisa da kuma mayar da mijin da mace ‘yar Najeriya ta auro a wata kasa shi ma ya zama dan Najeriya da sauran su.

Koken da suke yi dai ya bayyana rashin saka mata a harkar siyasa duba da cewa matan ne kusan kashi 65 cikin dari dake kada kuri’a a Najeriya.

Amma sun zama kamar ‘yan amshin shata a kasar kamar yadda ‘yar gwagwarmaya nan kuma mai fatufutukar nemawa mata da kananan yara ‘yanci Hajiya Maryam Mamman Nasir ta bayyana a hirar da ta yi da Muryar Amurka.

Hajiya Maryam ta kara da cewa mata a Najeriya sun farga sun kuma zama tsinstiya madaurinki daya tare da daura damarar fafutukar neman ‘yancin su.

‘Yar gwagwarmayar ta ce ko a babban taron jam’iyya mai mulki ta APC mata ba su amfana da komai ba inda ta ce duk a cikin mukamai 78 da aka bayar 11 ne kawai mata kuma mukamin da aka ba su ba wasu muhimman mukamai ba ne da suke nuna ana damawa da su a harkar.

Ta ce matsayar mata suka tsaya takarar shugabancin kasa kuma aka hana su to za su fito ba’a inuwar kowace jam’iyya ba tunda majalisa ta ba da damar hakan.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

XS
SM
MD
LG