‘Yan Najeriya sun fara jan hankalin ‘yan takara dake neman rike madafun iko da su maida hankali wajen fadin irin ayyukan da za su yi, in sun yi nasarar zabe maimakon yin yarfe wa junansu a lokacin yakin neman zabe.
WASHINGTON DC - —
Ya yin da manyan zabuka a Najeriya ke karatowa, ‘yan takara kuma ke zafafa yakin neman zabensu, wasu ‘yan kasar sunce sun lura da cewa kusan dukkan ‘yan takarar sun fi mayar da hankali ne kan kalaman batanci ga abokan hamayyarsu.
Matsalolin rashin tsaro da talauci da rashin ilimi da sauran ababen more rayuwa su ya kamata ‘yan takarar su maida hankali wajen fayyace yadda za su magancesu. A cewar wasu mutane da wakiliyar Muryar Amurka Zainab Babaji ta zanta da su.
Daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, Garba Abari, ya ja hankalin ‘yan Najeria ne kan su guji tada rikici lokacin zabe.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5