Yayin da ya rage kasa da kimanin makonni biyu a gudanar da babban zabe a Najeriya, hukumomi da kungiyoyin cikin gida da na ketare na shirya tarukan mahawara a tsakanin 'yan takarar gwamnonin Jihohi da kuma masu neman shugabancin kasar.
Sai dai masana na bayyana kokwanto akan tasirin irin wadannan tarukan mahawara akan talakawa.
A zaben shekara ta 2007 ne aka fara shirya mahawara tsakanin 'yan takara a Najeriya tun bayan da kasar ta koma tafarkin demokaradiyya a shekarar 1999, inda masu neman shugabancin kasar a wancan lokaci suka fafata a tsakanin su.
Da shekarar zabe ta dawo an kuma shirya irin wannan mahawarar a shekara ta 2011 da 2015, sai kuma a kakar zabe ta bana inda hukumomi da kungiyoyin ciki da wajen Najeriya ke shirya mahawara har ma a matakin jihohi, domin bai wa masu neman gwamna damar baje kolin ga talakawa.
Dr Sa'idu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero Kano ya ce "tasirin sai a gaba za a gani, saboda abu ne da ba a saba ba," sannan a zabukan da aka yi a baya "bai tasiri kan cin zabe ko rashin cin zabe ba."
Ko a karsehn makon nan, hukumar gidan Radiyon BBC hadin gwiwa da wasu kafofin labaru na cikin gida sun shirya mahawara tsakanin masu takarar gwamnan Kano a 5 daga cikin Jam'iyyun kasar nan, wato Abdullahi Ganduje na APC, Salihu Sagir Takai na PRP, Mustafa Getso na NPM,Abba K. Yusuf na PDP, da kuma Maimuna Muhammad ta Jam'iyyar UPP.
Dukkanin 'yan takarar dai sun halarci mahawarar, in ban da Abdullahi Umar Ganduje na APC kamar yadda ya kauracewa makamanciyar wanann mahawara da Jami'ar Bayero ta shirya a kwanakin baya.
A yayin mahawarar dai 'yan takarar sun yi alkawuran kyautata rayuwar Jama'a a fannonin kiwon lafiya Ilimi , kasuwanci zamatakewa da ayyukan noma, kana daga bisani suka amsa tambayoyi.
Saurari cikakken rahoton da Mahmud ibrahim Kwari ya aiko daga Kano: