Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Najeriya: An Yi wa ‘Yan Jarida Bita Kan Watsa Labaran Zabe


Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa
Shugaban INEC Ya Gana Da Shugabani Da Daraktocin Hukumar Zaben Kasa

An gargadi manema labarai das u gujewa yin gaban kansu wajen bayyana sakamakon zabe da ga tashoshin kada kuri’a domin kaucewa kawo rikici dakuma rudani a cikin al’umma.

Wannan gargadin ya na kunshe ne a jawaban da aka gabatar a wajen taron bita wa manema labarai da kungiyar ‘yan jarida ta kasa da kuma hadin gwiwar hukumar zabe INEC suka shirya a Bauchi, don tunatar da manema labarai game da hakkokin daya rataya a kansu kan zaben da za a gudanar a kwanan nan a fadin Najeriya

Kasancewar ‘yan jarida na da muhimmiyar rawa da za su taka a zabubbukan da za a gudanar a kasa baki daya, ya zamo tilas a sake tunasar da manema labaran game da muhimman ayyukan da suka wajaba akansu na ganin sun taimaka zabubbukan sun gudana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya ta hanyar ba da sahihan labarai masu inganci.

Kwamrad Ibrahim Malam Goje, shine shugaban kungiyar ‘yan jarida na kasa a jihar Bauchi, ya yi bayanin makasudin taron. Inda ya ce ganin yadda gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki a Najeriya suka mayar da hankali don ganin an samu nasarar yin babban zaben kasar, hakan ya sa suka ka yakamata su tara rawar da ta dace.

Shi kuma anasa sakon ga mahalarta taron bitar, kwamishinan yada labarai na jihar Bauchi, Alhaji Umar Ibrahim Sade, ya yi tambihi wa ‘yan jaridan game da tabbatar da sahihancin labaru sannan ya ci gaba da cewa ‘yan jarida sun zama tamkar madubin al’umma, hakan ya zama wajibi akansu su zama masu tantance gaskiyar labara kafin su watsa.

Shi kuma, Kwamishinan zabe ta INEC a jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Ibrahim, ya yi bayani a hukumance dangane da shirin hukumar ta INEC dangane da gudanar da zaben. Ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka duk kayayyakin zaben da ake bukata ya shiga hannu.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG