Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce ta gano wani shiri da wasu ke kullawa na kawo hargitsi a zaben kasar da za a nan da wasu kwanaki.
Najeriya na shirin gudanar da babban zabenta a ranar 16 ga watan nan na Fabrairu a duk fadin kasar.
Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Lt. Janar Tukur Buratai ne ya bayyana cewa sun samu wasu bayanai kan yadda wasu “marasa kisihin kasa” ke kokarin su kawo cikas a wasu sassan kasar a lokacin zaben.
Bayanan a cewar Buratai, sun nuna cewa za a hada kai ne da wasu ‘yan kasar waje wajen ta da husuma a wasu sassan Najeriyar.
Janar Buratai ya bayyana hakan ne yayin bude wani babban taron rundunar sojojin kasa na Najeriya a Abuja a jiya Litinin.
“Bari na fada a daidai wannan lokaci cewa, mun samu bayanai kan yadda wasu kungiyoyi marasa kishin kasa, wadanda ke samun goyon bayan wasu ‘yan kasar waje, kan cewa za su kawo hargitsi a zaben 2019 a wasu sassan kasar nan.” Inji Buratai.
Sai dai rundunar sojin ta Najeriya ta yi gargadin cewa, za ta ladabtar da duk wani dan kasa ko dan kasashen ketare da ta samu da hannun a yunkurin kawo cikas a zaben na Najeriya.
Saurari cikakken rahoton daga Hassan Maina Kaina: