A Uganda 'yansanda sun tarwatsa ofishin lauyoyin tsohon Firayim Ministan kasar

Amama Mbabazi tsohon Firayim Ministan Uganda da ya tsaya takarar shugaban kasa

'Yansandan Uganda sun farma ofishin lauyoyin tsohon Firayim Ministan kasar Amama Mbabazi wanda ya kalubali sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi 18 ga watan Fabrairu a kotu.

Tsohon Firai ministan Uganda, Amama Mbabazi, ya ce ‘yan sandan kasar sun kai samame a ofisoshin lauyoyinsa, inda suka kwashe na’urarorin kwamputa da wasu takardu da ke dauke da bayanan da shaidu suka gabatar, kan irin magudin da aka tafka a zaben kasar da aka yi ranar 18 ga watan Fabrairu.

Shi dai Mbabazi yana kalubalantar sakamakon zaben da ya ayyana Shugaba Yuweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya shigar da kara a kotun.

A jiya Laraba tawagar lauyoyin ya kamata su bayyana a gaban kotu, domin gabatar da hujjojin cewa an tafka magudi a zaben, amma samamen da aka kai ofishin lauyoyin nasa ya dagula al’amura a cewar Mbabazi

Ya ce da farko hakan na nufin ba za su iya cimma wa’adin da kotu ta basu ba, tunda an kwashe takardun da za su gabatar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce sun ga wasu mutane sanye da kayan ‘yan sanda, wadanda suka balla kofar ofishin lauyoyin suka kwashe kayayyakin da ke ciki.