Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Musuveni Ya Lashe Zaben Uganda


Hotunan shugaba Museveni na Uganda, wand aya lashe zaben shugaban kasa
Hotunan shugaba Museveni na Uganda, wand aya lashe zaben shugaban kasa

Shugaban kasar Uganda Yuweri Musveni ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, bayan da ya samu kashi kusan 61 na kuri’un da aka kada.

Shi kuwa abokin hamayyar Musuveni Kizza Besigye ya samu kashi 35 ne yayin da daya tankarar mai suna Amama Mbabazi ya samu kashi 1.4.

Akalla kashi 63 na masu kada kuri’a ne suka je rumfunan zabe a cewar hukumar zaben kasar wacce ta bayyana sakamakon na karshe.

An fidda wannan sakamakon zabe ne sa’o’i kadan, kafin karewar wa’adin bayyana shi ya cika.

Wani mai sa ido daga kungiyar tarayyar kasashen Turai, ya ce mamaye gurbin siyasa da jam’iyya mai mulki ta yi ya tasiri akan zaben, kana ya yi zargin cewa hukumomi sun yi barazana ga masu zabe da ‘yan takara a ranakun zabe da kuma kwanakin da suka biyo baya.

Rahotanni na nuni da cewa an yiwa Besigye daurin talala saboda zaman dardar da ake yi a kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG