A Tabbata An Yi Wa Nnamdi Kanu Adalci – Kungiyar Igbo Ta Duniya

Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB (AFP)

Kazalika sanarwar ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya, da ta tashi tsaye ta kare Nnamdi kanu wanda dan kasarta ne.

Kungiyar Al’umar Igbo ta Duniya WIC, ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su tabbata an gudanar da shari’ar Nnamdi Kanu daidai da yadda dokar kasa da kasa ta tsara wacce ta tanadi kare hakkin bil adama tare da kare lafiyar mutum.

A ranar Talata hukumomin Najeriyar suka sanar da cewa sun kama Nnamdi Kanu, wanda suke tuhuma da laifin cin amanar kasa baya ga wasu laifuka.

Har ya zuwa yanzu hukumomin Najeriyar ba su fadi inda suka kama shi ba.

“Mun samu tabbacin cewa an kama Nnamdi Kanu wanda dan kasar Birtaniya ne.”

“Hakan ya sa kama shin da aka yi ya saba ka’idar da aka tanada kan yadda za a mayar da mutum wata kasa.” In ji sanarwa da kungiyar ta WIC ta fitar sanye da sa hannun kakakinta Basil Onwukwe da shugabanta Prof. Anthony Ejiofor.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa, da paspo din Birtaniya Kanu ya yi tafiya.

“A dalilin haka,” kungiyar ta ci gaba da cewa, “muna kira ga gwamnatin Najeriya, da ta tabbata an tafiyar da shari’ar Nnamdi Kanu yadda dokar kasa da kasa ta tsara wacce ta tanadi kare hakkin bil adama tare da kare lafiyar mutum.”

Kazalika sanarwar ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya, da ta “tashi tsaye ta kare dan kasarta, sannan akwai bukatar gwamnatin Birtaniya ta yi bincike ko akwai sa hannun wata kasa a wannan turka-turka.”

Kungiyar ta WIC, ta kuma yi kira ga Amurka da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya “da su sa ido kan yadda ake take hakkin bil adama a Najeriya ciki har da wannan batu na kama Nnamdi Kanu.”

WIC har ila yau ta zargi gwamnatin Najeriya kan yadda take “nuna banbancin ta hanyar rarrashin ‘yan Boko Haram da Fulani makiyaya” yayin da ake daukan tsauraran matakai akan al’umar Igbo, inda ake ba da umarnin a harbe su.

Sai dai a karshe sanarwar ta ce, “dukkan al’umar Igbo da ke ko ina a duniya su kwantar da hankalinsu. Dole ne a kare ‘yancin Igbo, kuma ba za a rika tankwasa su ba.”

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Biafra, DSS, IPOB, Binta Nyako, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Nigeria, da Najeriya.

A ranar Talata aka gurfanar da Kanu a gaban wata kotu da ke Abuja, wacce ta ba da umarnin a tsare shi a ofishin hukumar tsaro ta DSS.

A cewar Malami, ana zargin Nnamdi Kanu da karya dokar belin da aka ba shi, da tunzura mutane su yi bore ta hanyar yada labarai ta kafar rediyo, talabijin, da kafafen yanar gizo na a kai hari kan gwamnatin Najeriya da gine-ginenta.

Ya kara da cewa ana kuma zarginsa da laifin ta da zaune tsaye a kudu maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula, sojoji, da sauran jami’an tsaro, da suka hada da ‘yan sanda.

A shekarar 2017 aka ba da belin Nnamdi Kanu bisa dalilai na rashin lafiya, amma Kanu ya tsallake belin ya fita kasar waje, bayan wani samame da sojojin Najeriya suka kai gidansa.

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa Nnamdi Kanu ya fada a zaman kotun da aka yi ranar Talata cewa, ya gudu ne saboda ana yi wa rayuwarsa barazana.

A ranar 26 ga watan Yuli za a ci gaba da shari’ar ta Nnamdi Kanu.

Nnamdi Kanu: ​An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Your browser doesn’t support HTML5

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi