A Shekara Ta Biyu A Jere, Yawan Dukiyar Shugaba Donald Trump Ta Ragu Da Daruruwan Miliyoyi

Dukiyar shugaban Amurka Donald Trump ta ragu da dala miliyon 400 a bara, ta komo dala biliyan uku da miliyan dari, lamarin da ya sa mutane har 222 suka shige gabansa a cikin jerin attajirai na duniya da suke da dukiyar da ta kai akalla dala biliyan kamar yadda Mujallar Forbes take aunawa kowace shekara. Jeri na baya-bayan nan ya fito jiya talata.

Trump ya fado daga matsayin mutumi na 544 da yafi yawan dukiya a duniya a shekarar 2017, ya komo na 766 a wannan shekara ta 2018. Wannan ita ce shekara ta biyu a jere da dukiyar Trump take raguwa.

Sauka kasa da Trump yayi a cikin jerin mutanen da suka fi arziki a duniya, tana zuwa ne a daidai lokacin da a karon farko aka samu karin mutane har 35 da suka shiga cikin jerin masu dukiyar Biliyan na mujallar Forbes.

Mai kamfanin kasuwancin yanar gizo na Amazon Jeff Bezos, shine mutumin da yafi kowa kudi a duniya kuma dukiyarsa ta kai dala biliyan 112, wato karuwar dala biliyan 39 da miliyon dari biyu kan abinda ya mallaka a shekarar da ta gabata. Mutane biyu da suke biye dashi sune Bill Gates mai kamfanin Microsoft wanda dukiyarsa ta kai dala biliyan 90, sai kuma mai zuba jari Warren Buffet wanda keda kudi dala biliyan tamanin 80.

Mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Turai kuma na hudu a cikin jerin masu kudi a duniya shine mai kampanin sayar da kayan alatu na LVMH, Bernard Arnault, wanda dukiyarsa ta kai dala biliyan 72.

Amurka ta fi kowace kasa yawan attajirai masu biliyoyin daloli a duniya, wadanda yawansu ya kai 585, sai kuma kasar China.

Jihar California ta Amurka kadai tana da attajirai masu biliyoyin dala har mutum 144, kuma jihar kadai tafi kowace kasa yawan attajirai a duniya, baicin Amurka da China.

Ita kuwa kasar Jamus tafi kowace kasa a nahiyar Turai yawan attajirai masu akalla biliyan, wadanda yawansu ya kai 123. India kuma tana da attajirai da yawansu ya kai 119 sai kuma kasar Rasha ke bi mata da attajirai 102.

Kasashen Hungary da Zimbabwe sun shiga jerin kasashe masu attajirai dake da biliyan a karon farko kuma dukkaninsu nada mutum guda.

Mutane goma na Saudi Arabia da sunayensu ke yawan bayyana a cikin jerin attajirai guda dari da suka fi arziki a duniya, ciki har da babban dan kasuwa mai kere kere, Yarima Alwaleed bin Talal, an fidda su a cikin sunayen na bana, sakamakon rashin tabbas a kan abin da suka mallaka yanzu, bayanin Forbes ya biyo bayan yaki da rashawa da gwamnatin Saudi Arabia take yi a cikin wannan lokaci da ake shirya sunayen.

A karon farko a tarihi, jerin sunayen wadanda suka fi arziki a duniya, suke da akalla dala biliyan daya, a bana ya kunshi mata su 256, wadda Alice Walton, magajiyar dukiyar kamfanin Walmart, take kan gaba da zunzurutun kudi dala biliyan 46.

A cewar mujallar Forbes, attajirai dubu biyu da 208 da sunayensu suka bayyana a cikin jerin sunayen da ta fitar a wannan shekara, idan aka hada kudadensu baki daya sun kai dala triliyon tara da biliyon dari daya, wanda ya kai a kalla kashi hudu cikin dari na arzikin duniya baki daya.