A Nijar Kotu Ta Yanke Hukunci kan karar Bangarorin Jam'iyyar MNSD

Shugaban Nijar Mahamadou Isoufou

A zamanta da tayi jiya a Niamey ko Yamai kotun daukaka kara ta tabbatar da Alhaji Seini Umar a matsayin halartaccen shugaban jam'iyyar MNSD Nasara kenan abokin hamayya Albade Abuba sai ya hakura

Kotun daukaka kara ta birnin Niamey ta bayyana jagoran ‘yan adawar jamhuriyar Nijer ALHAJI SEINI UMARU a matsayin ‘yantaccen shugaban jam’iyar MNSD NASARAbayan da aka shafe shekaru biyu ana tafka shara’a tsakaninsa da ministan musamman a fadar shugaban kasar Nijer ALBADE ABUBA.

Irin yadda magoya bayan Seini Umaru ke murnar nasarar da suka samu kenan jim kadan bayan da kotun daukaka kara ta birnin Niamey ta bayyana hukuncin da ta yanke a game da shara’ar da ta hada su da bangaren ALBADE ABUBAyau shekaru sama da biyu kenan . ALBDULKADRI TIJANI jigo a bangaren Neini Umar dake bayyana farin cikinsa cewa yayi kofa bude take ga wadanda ke tunanin komawa gida

ALHAJI IBRO AYUBA sakataren watsa labarei a bangaren ALBADE ABUBA na mai cewasun yi na’am da wannan hukunci.

Wasu rahotanni sun ce bangaren na Albade Abuba na gab da kafa wata sabuwar jam’iyar siyasa to amma suka musanta hakan. A watan Agusta shekarar 2O13 ne rarrabuwar kawuna ta kunno kai tsakanin bangaren SEINI UMARU da na ALBADE ABUBA bayan da shugaban kasar Nijer ISUHU MAHAMADU ya bayyana shirin kafa gwamnatin hadin kan ‘yan kasa.

Ga rahoton Souly Mummuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

A Nijar Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Bangarorin Jam'iyyar MNSD - 2' 20"