Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canjin Gwamnan Diffa: Kura Na Cigaba Da Tashi


Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou

Bayan tsige gwamnan jahar Diffa, inda 'yan bindiga su ka kashe wasu mutane da dan dama, kura na cigaba da tashi saboda da banbancin ra'ayi.

Bayan zaman Majalisar Ministoci, wanda shi kuma ya biyo bayan kashe wasu mutane da dan dama ne aka Canza gwamna Yakuba Sumana Gawo na jahar Difa mai fama da matsalar tsaro, aka maye shi da wani soja kuma tsohon Minista, Janar Abdu Kaza, cewar wakiliyarmu a Damagaran Tamar Abari.

Tuni dai jama’a, wadanda su ka bukaci a sakaya sunayensu, su ka fara bayyana ra’ayoyinsu ciki har da wani mai cewa ya san Janar Abdu Kaza sosai mai sanayyar makamin aiki ne saboda ya rike makamai da yawa. Mutum na biyu kuma cewa yak e tun dama kamata ya yi a nada soja saboda matsalar tsaro da ake samu. Mutum na uku kuwa cewa ya yi ba don wani kishin kasa aka canza gwamnan ba sai don kawai takaddamar wasu mutane da kuma nuna isa da aka nuna ma daya bangaren.

Ya ce gas hi baya nan ma ya na can wajen aikin Hajji aka tunbuke shi aka nada wanda ake so. Shi kuwa mutum na hudu cewa ya yi a yanayin tabarbarewar matakan tsaro irin haka, soja ya fi dacewa da zama gwamnan jaha. Don haka, ya ce abin da aka yi ya dace. Tamar ta yi kokarin jin abin da doka ta ce game da canjin gwamna da kuma mai ikon yin hakan, to amma bayan da wani masanin doka ya yi alkawarin bayani, daga baya kuma sai ya noke. Tamar ta ce sai dai kamar jahar Diffa, jahar Agadez ma gwamnanta soja ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG