A Na Ci Gaba Da Shara'a Kan Makomar Janar Salou Souleymane

Alkalan kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar

Alkalan kotun tsarin mulkin Jamhuriyar Nijar

Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta fara zaman shari’ar da ke tsakanin gwamnatin kasar da Janar Salou Souleyman wanda aka garkame a gidan yari a watan Disamban 2015 tare da wasu hafsoshin soja da fararen hula a bisa zargin yunkurin juyin mulki, zargin da suka sha musantawa.

A zaman gaggawar da Kotun ta yi a ranar 24 ga watan Oktoban 2023, ta bada umurnin a sallami dattijon hafsan ya koma cikin iyalinsa a matsayin afuwar da doka ta yi tanadi wa firsinonin da suka manyanta, saboda dalilai masu nasaba da yawan shekaru, sai dai matakin bai yi wa mahukunta dadi ba mafari kenan suka daukaka kara.

Hafsan sojan sama Janar Salou Souleymane wanda a watan Janerun 2018 kotun hukunta laifikan soja ta yanke masa hukuncin zaman wakafin shekaru 15 tare da wasu sojoji 11 da wasu fararen hula sama da 10, da tace ta samu da hannu a yunkurin kifar da shugaba Issouhou Mahamadou a watan Disamban 2015, ya bukaci kotu ta sallame shi a matsayin afuwar da doka ta yi tanadi ga firsinonin da suka manyanta kasancewarsa dan shekaru 70 a duniya, mafari kenan alkalin kotun Tribunal ya bada umurni a sallame shi sakamakon cika sharuda.

Kotun Nijar

Kotun Nijar

Sai dai hukuncin bai yi wa gwamnatin Nijar dadi ba, sabili haka ta daukaka kara zuwa kotu ta gaba wace ta yi zama a yammacin Laraba.

Bayan tafka mahawwara ta fiye da sa'a 1, lauyansa Maitre Mohamed Hamani Salim yace, "mun isar da sakon gaskiya, domin mu aikinmu shine mu fayyace gaskiyar abinda doka ta fada. Shi kuwa alkali shi ke da alhakin yanke hukunci dai-dai da doka, sannan su kuma masu alhakin zartarwa su yi nasu aikin.

Ina tuna maku cewa tun tuni alkali ya yanke hukunci domin a baya ya bada umurni a sallami Janar salou Souleymane take yanke, duk kuwa da cewa akwai damar daukaka kara amma duk da haka ana ci gaba da tsare shi a gidan kaso ba tare da wata kwakwarar hujjar doka ba."

Daruruwan ‘yan uwa da aminnan Janar Salou Souleymane ne suka hallara dakin shara’ar da nufin bai wa wannan hafsan sojan sama goyon baya. A cewarsu suna da kwarin gwiwar alkali zai yi na’am da hukuncin kotun da ta sallame shi a matakin farko kamar yadda wani dan uwansa Ali Maiga ya bayyana.

Lauyoyin da ke kare bangaren gwamnati ba su so su yi wa manema labarai bayani ba a karshen wannan zama. Yanzu dai alkali ya ayyana ranar 22 ga watan nan Nuwamba a matsayin ta sanar da hukuncin da zai yanke a wannan shara’a da ke daukan hankalin jama’a.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

A Na Ci Gaba Da Tafka Shara'a Kan Makomar Janar Salou Souleymane