Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Shari'a A Nijar Sun Yi Barazanar Kama Masu Yada Kalaman Tunzura Jama'a


Kotu
Kotu

Babban alkali mai shigar da kara a kotun daukaka kara ta birnin Yamai ya yi kashedi ga wasu wadanda ya ce suna yada labarai da kalaman da ke barazanar ta da fitina a wani lokacin da ake matukar bukatar ganin ‘yan Nijar sun kasance tsintsiya madaurinki daya.

NIAMEY, NIGER - Babban alkalin ya yi tunatar wa akan hukunce-hukuncen da doka ta yi tanadi ga duk wanda aka kama da yada irin bayanan da ka iya ta da hankalin jama’a.

A wani taron manema labaran da ya kira, babban alkali mai shigar da kara a kotun daukaka kara Procureur General Ma’azou Oumarou, ya fara da cewa “mun lura da yadda ake tsananta yada wani sabon nau’in bayanai a kafafen sada zumunta da kafafen labarai da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma.”

Ya ce abin mamaki ne a dai-dai lokacin da kasa ke bukatar hadin kan ‘ya’yanta, wasu mutane sun dukufa da yunkurin maida hannun agogo baya a ci gaban da aka samu da nufin jefa kasar cikin tashin hanakli.

Ya kara da cewa, “ba za mu rufe ido kan wannan sabon salon ‘yancin fadin albarkain baki da ke baza kwayoyin rarrabuwar kawuna da tursasa wa kasarmu ba.”

Alkalin ya tunatar da masu irin wannan danyen aiki cewa Nijar ta tanadi dokoki masu tsauri akan duk wanda aka kama da laifika kamar cin amana da leken asiri da barazana ga tsaron kasa da kai hari wa kasa ko kuma hada kai a irin wannan yunkuri da yi wa kasa zagon kasa ko shiga cikin wata hatsaniyar bijirewa hukuma.

Ya kuma kara da yin tunatar wa kan tanade-tanaden dokokin hukunta masu amfani da kafafen sada zumunta.

Kungiyar ABC ta masu fafutuka ta yanar gizo wato Blogeur, ta bayyana gamsuwa da wannan mataki in ji wani jigonta Mamoudou Djibo Hamani wanda ya ce “cikin farin ciki muka karbi sanarwar babban alkali mai shigar da kara a kotun Yamai domin sanin kowane cewa tun a washegarin juyin mulkin da ya hambarar da gwamantin Jamhuriya ta 7 a ranar 26 ga watan Yuli wani sabon jinsin masu amfani da kafafen sada zumunta ya dukufa da yada kalaman tayar da zaune tsaye da na nuna jihanci da bambancin kabila sabanin abubuwan da dokokin kasa suka yi tanadi.”

Sakataren gamayyar kungiyoyin ‘yan jarida, Souleymane Oumarou Brah, ya yi amanna akan yanayin rudanin da kafafen sada zumunta suka haifar a ‘yan makonnin nan, inda ya yi hannunka mai sanda game da abin da ka iya zama makomar aikin jarida a nan gaba.

Dambarwar da ta barke a tsakanin gwamnatin mulkin sojan Nijar da a wani bangaren kungiyar CEDEAO sakamakon juyin mulkin 26 ga watan Yuli, wani al’amari ne da a yanzu ya fara shafar aikin jarida ganin yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar goyon bayan manufofin sabbin mahukunta ke farwa manema labarai musamman wadanda suka shigo daga kasashen ketare.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Shari'an Nijar Sun Yi Barazanar Kama Masu Yada Kalaman Batanci.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG