A Kafa Doka Mai Tsanani Domin Ilimantar Da Yara

A wani kira da sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa'adu Abubakar ya yi a sakon sa na barka da sallah, ranar juma'a da ta gabata na cewar ya kamata hukumomi da gwamnatoci su fitar da doka da zata hukunta duk iyayen da suka hana 'ya'yan su zuwa makaranta domin neman ilimi. wakilin sashen Hausa da ke birnin Sokoto Murtala Faruk Sanyinna ya yi hira da Ibrahim Jarmai inda ya yi karin bayani kamar haka;

Gaskiya ne tun da farko masu nazari akan al'amura da masana daban daban sun yi ta bayyana yadda arewacin Najeriya ke samun koma baya a harkokin ilimi da sauran su musamman idan aka kwatanta yankin da sauran sassan kasar.

Yara da dama suna lalacewa a sakamakon rashin ilimi, wannan yana daya daga cikin abubuwan da suka ja hankalin mai alfarma sarkin musulmi kenan har ya yi wannan kira ga gwamnatoci da su kafa sabuwar doka domin hukunta iyayen da suke hana 'ya'yan su zuwa makarantar boko.

'Yan siyasa a wurare daban daban sun yi kokarin gina makarantu domin taimakawa harkokin ilimi amma jama'a da dama har yanzu ba su ba abin muhimmanci ba. Wannan da daya daga cikin dalilan da yasa sarkin musulmi ya yi wannan kiran, "ga makaratu an kawo wa jama'a har gida amma da dama sun hana yaran su zuwa, alhali ilimi abu ne da ake sa kudi a nema kuma ga shi an kawo shi har gida kuma kyauta".

Za'a iya fuskantar kalubale da dama a sakamakon yadda wasu iyaye ke dogara kan 'ya'yan su wajan gudanar da wasu ayyuka wanda dalilin haka ne ma yasa iyaye da dama ke hana 'ya'yan su zuwa makaranta.

Ga karin bayani.