Akalla yara kanana arba'in da bakwai suka mutu, wasu arba’in kuma sun warke daga masassarar, a halin yanzu yara ashirin na asibiti ana masu jinya, a cewar Malam Abubakar, wakilin mai unguwar kauyen Gidan Dugus, na gundumar Wangara a karamar hukumar Dutse.
Daya daga cikin yaran da suka murmure daga cutar, mai suna Sahura Bashir ta bayyana cewa maganin gargajiya aka bata kafin daga baya aka kai ta asibiti.
Malama Khadija kuwa da ta rasa danta daya tak sanadiyar cutar, ta ce da suka je asibiti an bayyana mata cewa danshi ya kama yaron, bayan kwana biyar yaron ya rasu.
Malam Bashir Usman Gidan Dugus ya ce a rana daya sun rasa ‘yaya uku a gidansu. Ya kuma ce ko shagon saida magani basu da shi balle ma asibiti.
Wakilin mai unguwa malam Abubakar ya ce a halin yanzu addu’a suke Allah ya kawo saukin wannan cuta. Ya kuma ce ba a sanar da hukuma gameda wannan cutar ba akan lokaci sai daga baya, daga nan hukumomin yankin suka tura masu bincike.
Alhaji Adamu Aliyu Rungumau, mataimakin shugaban karamar hukumar Dutse, ya fadi cewa bayan samun wadanna bayannan sun tura likitoci don su gargadi al’ummar garin akan muhimmancin tsabtar jiki da muhalli don kariya daga wannan annoba. A cewar sa gwaje-gwajen da aka yiwa wasu daga cikin yaran sun nuna cewa suna dauke da cutar cizon sauro da ake kira Malaria da turani.
yanzu haka iyayen yaran na cikin yanayin dimuwa da ban tausayi, domin kuwa yayinda wasu yaran ke samun sauki, wasu kuma suna kamuwa da cutar, a cewar wakilin sashen hausa Mahmud Ibrahim Kwari da ya kai ziyara garin.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5