Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani Kan Kasafin Kudin Shekarar 2018


‘Yan Najeriya na ci gaba da mayar da martani dangane da kasafin kudin Naira Triliyan Takwas da digo shida, da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a gaban ‘yan majalisar dokokin kasar.

Kamar yadda aka gani, kasafin kudin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar jiya Talata a gaban majalisar dokokin kasar ya zarce na shekarar da muke ciki, lamarin da yasa ‘yan kasar da dama ke tofa albarkacin bakin su, kamar yadda wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka ya jiyo ra’ayoyin jama’a.

Sai dai kuma a cewar masana tattalin arzkin kasar, Alhaji kasimu Garba kurfi, masanin tattalin arziki da zuba jari dake jihar Legas, ya ba bayyana kasafin kudin ke da wuya ba, amma yadda za’a yi amfani da shi.

Malamin ya kuma kara da cewa lokaci yayi da ‘yan majalisun dokokin Najeriya, zasu mayar da hankali wajan ba gwamnatin tarayya damar gudanar da manyan ayyuka, sauran ayyukan su na mazabu a barwa jihahi da kananan hukumomi, ta haka ne kadai ‘yan Najeriya zasu gani a kasa.

Masanin tattalin arzikin ya kara da cewa har ila yau akwai matsala domin idan aka yi la’akari da yadda kasar zata biya bashin kudi kusan fiye da Triliyan Biyu, da ake bin kasar musamman bashi na cikin gida.

Kamar sauran ‘yan Najeriya, shima shugaba Muhammdu Buhari ya yi kira ga ‘yan majalisar da su gaggauta amincewa da wannan kasafin kudin domin a fara aiki da shi a watan Janairun shekara mai zuwa, ganin yadda har yanzu ake ci gaba da jani-in jaka akan kasafin kudin bana, duk da cewa shekarar na dab da karewa.

Domin karin bayani saurari rahoton Babangida Jibrin daga Legas.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG