Kungiyar a wajen wani babban gasar karatun Alkur’ani na kasa da kasa da aka gudanar a Yola,masana da kuma hukumomi sun bayyana muhimmancin karatun allo,musamman a wannan lokaci na lalacewar tarbiya,koda yake sun ce akwai wani hanzarin da ba gudu ba ne.
Duk da cewa abubuwa sun sauya,da alamun da saurar rina a kaba game da batun tura yara almajiranci da iyaye keyi musamman a arewacin Najeriya,batun da ya sa yanzu hukumomi dama wasu kungiyoyin addini yunkurowa domin fadakar da al’umma illar dake akwai a yawon almajirancin,yayin da tuni wasu malaman tsangaya suka sauya salo domin tafiya da nizami ga almajiran .
Karatun tsangaya wani tsarin koyar da al’ummar musulmi ne wanda ke da dadadden tarihi sama da shekara dubu, kuma wannan tsarin koyo da koyarwa ya fara yaduwa a arewacin Nijeriya ne tun kafin zuwan turawa, kuma ko da Turawan suka shigo kasarnan, sun iske jama’ar arewacin Nijeriya da tsarin koyo da koyarwa ta hanyar karantarwar alkur’ani
To sai dai kuma daga baya an samu sauyi batun da masana ke cewa dole a tashi tsaye.
Da yake jawabi game da matsalar almajiranci a Najeriya, Shehun Malami,kuma shugaban majalisar malamai na kungiyar IZALA a Najeriya Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir yace dole a hada hannu.
Shehun Malamin wanda ke jawabi a wajen wani babban taron gasar karatun Al-qur’ani wato musabaka na ciki dama wajen Najeriya da kungiyar ta shirya a Yola,malamin wanda ya yaba game da matakan da hukumomi suka soma dauka a yanzu na gwama karatun allo dana bokon, yace akwai abun dubawa.
Shima dai a jawabinsa,gwamnan jihar Adamawa Senator Muhammadu Bindo Jibrilla wanda yace gwamnati a shirye take wajen habaka harkar karatun al’Qur’ani ya nemi afuwar al’umman jiharsa game da abubuwan dake faruwa inda har wasu ke danganta shi da wani bangare.
Kamar yadda alkalumman asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ke ma nunawa,dubban yara ne ake raba su da iyayensu da sunan zuwa karatun allo,wanda sau tari wasu kan bige da yawon bara,batun da masana ke cewa dole a tashi tsaye.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani
Facebook Forum