Kimanin mutane 40 ne ake zarginsu da aikata ayyukan ta’addanci ko kuma hada baki da masu tada kayar baya.
A karon farko an dage shari’ar daga birnin Yamai zuwa Diffa inda rikicin Boko Haram ya yi kamari domin ragewa dangin wadanda ta’addancin ya shafa wahalar yin bulaguro zuwa Yamai domin su saurari karar.
A wannan karon alkalai uku ne zasu saurari kararraki har guda 20 yayinda aka tanadi lauyoyin da zasu kare wadanda ake tuhuma.
Mai shigar da kara a madadin gwamnatin Niger Sha’aibu Salma ya ce za’a yi shari’ar akan adalci da gaskiya. Za’a yi shari’ar a bayanai
‘Yan uwa da dangin wadanda suka fada hannu mahukumta sanadiyar zargin cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun goyi bayan zaman dari bisa dari saboda akwai masu laifi akwai kuma wadan da basu da laifi. Suna da karfin gwuiwar cewa duk wadanda basu da laifi za’a sake su.
A saurari karin bayani a rahoton Souley Barma
Your browser doesn’t support HTML5