Wasu mayaka dauke da bindigogi da kayan fashe-fashe, sun kai hari kan wata hedikwatar rundunar sojin kasashen wani yanki na Afirka wadda ke tsakiyar kasar Mali, su ka hallaka sojoji biyu da kuma wani farar hula.
Maharan sun tayar da bama-baman da su ka jibga cikin wata mota inda su ka lalata mashigar hedikwatar sojojin kungiyar kasashe biyar ko G5 na yankin Sahel, sannan su ka shiga ciki su ka yi ta bude wuta.
Rundunar ta G5 Sahel sojojin gamayya ne na kasashen Afirka da ke yankin Sahel, wadda aka kafa bara saboda ta yaki masu da'awar jahadi. Rundunar ta kunshi sojoji 5,000 daga kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Janhuriyar Nijar.
Ciyaman din kungiyar, Shugaba Mahammadou Issoufou na Janhuriyar Nijar, ya tabbatar da adadin mace-macen. Jami'ai a Mali sun ce su ma maharan an kashe biyu daga cikinsu a musayar wutar da aka yi.
Facebook Forum