Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Bai wa Dan Issoufou Mahamadou Mukami Ya Janyo Cece-Kuce


Shugaba Mahamadou Issoufou
Shugaba Mahamadou Issoufou

Nada Mamman Sani Issoufou Mahamadou a sahun masu tafiyar da harkokin Fadar Shugaban Kasar Nijar a yayin wa'adin mulki na biyu na Shugaba Isoufou al'amari ne da ya daure wa jama'a kai saboda abu ne da ba a saba gani ba a tarihin kasar.

"Ba mu taba samun wanda ya dauko dan cikinsa ya sa a cikin harkar iko a tarihin Nijar. Mutum don kawai yana danka sai ka dauko shi yana yaro karami ka dora a matsayin mataimakin darektan fadarsa?" inji jigon kungiyoyin kawancen da ke adawa da dokar harajin 2018.

Wani tsohon dan majalisar dokokin kasa daga Jam'iyyar PNDS Tarayya, Abdulmumini Usman, ya mayar da martanin cewa, kamar yadda duk dan Nijar ke da hakkin rike wani mukami ko wani aiki, shi ma Mamman Sani Issoufou na da hakkin yin haka, koda ya ke dan shugaban kasa ne. Sannan kuma ya cancanci rike mukamin da aka ba shi.

"A kowane mako za ka ji shugaban kasa yayi nade-nade. To don ya nada dansa sau daya a cikin shekaru da shekaru, bai kamata a ce ya zama abin korafi ba," inji Usman.

Bayan zaben shugaban kasa a 2016 ne Shugaba Mahamadou Issoufou ya nada dansa Mamman Sani da aka fi sani da Abba a matsayin mai ba shi shawara a fannin sadarwa kafin ya mayar da shi mataimakin darektan fadarsa a makon da ya gabata, wanda wasu 'yan Nijar ke ganin cewa wani matakin shigar da yaron cikin harkokin siyasa dumu-dumu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG