Yau Juma'a kungiyar Amnesty ta gabatar da wannan rahoto daya baiyana dala dalan bayanin data samu daga hirarrakin data yi da tsaffin fursunonin gwamnati dana 'yan aware.
Kungiyar Amnesty tace bayanan data samu sun firgita ta. Domin mutanen da aka yi hira da su sun ce akan rataye su da kafa ko a hannun su, su yin barci na wasu kwanaki ko kuma ayi barazanar cewa za'a kashe su.
Rahoton sun ce fursunoni sun baiyana yadda aka yi ta dukan su, ko gallaza masu ta hanyar amfani da karfin wutar lantarki ko kuma a sossoke su da wuka, ko kuma ayi musu kisan yaudara.
A saboda haka kungiyar Amnesty ta yi kira ga hukumomin Ukraine da sun binciki wadannan zarge zargen laifuffukan yakin da wasu muggan abubuwa da aka yi, kuma a hukunta duk wanda aka samu da laifi.