Yace rashin sanin tabbas, hade kuma da rashin wani matsayi yana daya daga cikin abubuwan da suka sa mutane suna arcewa. Mr. Blinken yayi wannan furuci ne yau Juma'a a birnin Yangon inda ya zanta da jami'an kasar Myanmar.
Mabiya addinin Budda na kasar Burma sun hanawa Musulmi zama yan kasa ana kuma tauye musu 'yancin su.
Kimamin yan gudu hijira da bakin haure dubu uku, yawancinsu yan Rohingya daga kasar Burma da Bangladesh ne aka ceto, ko kuma suka yi iyo zuwa gabatar teku a kasashen kudu maso gabashin Asiya.
A ranar Alhamis aka tsince kwale kwalen a gabar tekun jihar Rakhine inda dubban yan Rohingya ke arcewa daga musuguna musu da ake yi. Su kuma jami'an kasar Burma sunce akwai wasu 'yan kasar Bangladesh da su ke karyar cewa su yan Rohingya ne, domin su samu agaji daga Majalisar Dinkin Duniya.
Hukumomi a kasar Myanamar sun ce zasu bayar da taimakon jin kai, kuma za su tantance ainihin inda mutanen suka fito domin a maida su kasashen su.