Kwastam na martani kan zargin da kungiyar ‘yan gwanjo ta cigaba da yi ma ta na nuna hukumar na gwanjan kayan da ta kwace musamman motoci tamkar kyauta ga ‘yan lelen ta.
A takarda da ya gabatar da ke nuna tsarin yin gwanjan na motoci, mataimakin shugaban hukumar mai kula da shelkwata a Abuja, ACG Muhammad Abba Kura ya ce ta hanyoyi uku ne su ke yin gwanjan kuma hakan na bisa tanadin dokokin Najeriya ne.
ACG Kura ya ce su kan yi gwanjan motocin da gwamnati ta saya da kudin ta ne kadai in sun kai shekarun gwanjo ga ‘yan gwanjo amma motocin da aka kwace daga simoga da kuma wadanda masu su su ka gaza bayyana don fiton su har lokaci ya kure; shugaban hukumar ne kadai ke da hurumin zabar wadanda za a yi wa gwanjan.
Muhammad Kura ya musanta duk wani yanayi da wani zai yi zargin cewa motocin a kan yi gwanjan su ga ‘yan uwa da abokan arziki ne.
Shugaban kungiyar ‘yan gwanjan Abubakar Musa Kura ya bukaci hukumar ta kara duba doka don a cewar sa sabuwar doka, ba ta 1891 tun kafuwar kwastam ba, ta ba wa hukumar hurumin yin gwanjan dukan kaya ga ‘yan gwanjan.
A yanzu haka kwastam ta amsa gayyatar kwamitin bincike na majalisar dokokin Najeriya da ke duba batun zargin na rufa-rufa a gwanjan.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5