Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Masu Gwanjon Kayayyaki Ta Najeriya ta Nuna Damuwa Game Da Ayyukan Hukumar Kwastam


Shugaban Kungiyar Masu Gwanjon Kayayyaki Ta Najeriya
Shugaban Kungiyar Masu Gwanjon Kayayyaki Ta Najeriya

Kungiyar masu gwanjon kayayyaki ta Najeriya tayi zargin cewa hukumar hana fasa kwauri wato kwastam na saka son zuciya da almundahana game da yadda take gudanar da ayyukan ta.

A taron manema labaru a Abuja, shugaban kungiyar Alh. Musa Kurra Abubakar ya ce hukumar kwastam din bata yin aiki tare da su a matsayin su na abokan hulda duk da cewa sun cika duk wasu ka’idojin gwamnati.

Shugaban yace abubuwan da suke korafi akai sun hada da umurnin da shugaba kasa Muhammdu Buhari ya bayar na rufe iyakokin kasar nan don inganta noman shinkafa yana mai cewa bai yi nasara ba, sannan kayayyakin da aka kwace suna rubewa a hannun hukumar ba tare da an sayar dasu ba.

Alhaji Musa kurra ya kara da cewa hukumar hana fasa kwaurin tana yin gwanjon kayayyaki ba bisa ka’ida ba don wasu ‘yan gaban goshinta su amfana wanda yace hakan kamar zagon kasa ne ga cigaban kasa.

Da yake maida martini game da zargin, mukadaddashin kakakin hukumar hana fasa kwauri a Najeriya Abdullahi Aliyu Maiwada yace hukumar su na gudanar da ayyukanta ne bisa doka da oda.

Abdullahi Aliyu Maiwada, mukadaddashin kakakin hukumar hana fasa kwauri
Abdullahi Aliyu Maiwada, mukadaddashin kakakin hukumar hana fasa kwauri

Wannan dai ba shine karo na farko da yan kasuwa da masu safarar kayyaki ke kokawa da jamian na kwastan ba tun bayan umarnin rufe iyakoki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

XS
SM
MD
LG