A ranar 29 ga wannan wata na Mayu gwamna Lamido zai kammala wa’adinsa na biyu bayan da ya kwashe shekaru takwas yana mulkar jahar.
“Mulkin da zai yi na ‘yan Jigawa ne, zabe hanya ce kawai ta neman wannan mulki saboda haka Jigawa ce APC sa, idan ko Jigawa zai yiwa aiki, to ya kamata duk dan jahar ya bashi hadin kai ya yi masa addu’a.” Lamido ya ce.
Da aka tambaye shi sakonsa ga ‘yan jahar sai ya ce “sako na ga ‘yan Jigawa shi ne abin da aka yi min na ba da hadin kai shima sabon gwamna a yi mai haka domin abin da mu ke so shi ne mulkin Jigawa ya ci gaba.”
Game da fatan shi, gwamna Sule Lamido ya ce shi ne a samu wutar lantarki da ruwan sha a kowane kauye “ba sai an sa hula a masallaci.” ana neman taimako.
Tuni dai gwamna mai shirin karbar mulki ya ce gwamnatinsa za ta dora daga inda gwamna Lamido ya tsaya musamman ayyukan da ba a kammala su ba.
“Dole a ci gaba da abin da aka fara saboda kudin Jigawa aka dauka aka fara da su, babu hujjar a ce don wani ya fara abu kai ka soke, hakan ba daidai ba ne.” In ji Sabon gwamna Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar.
Ga karin bayani a rahoton Mahmud Kwari daga Jigawa:
Your browser doesn’t support HTML5