Jirgin Ruwan Farko Dauke Da Kayan Agaji Ga Al’ummar Gaza Ya Yada Zango A Al-Arish

CYPRUS-PALESTINIAN-ISRAEL-CONFLICT-AID

Jirgin ruwan mallakin kasar Turkiya, na makare da tan 871 na kayan agajin da suka hada da janaretoci 300 da bandakunan tafi da gidanka 20, da tantuna 10, 460 da kuma barguna 14, 350, a cewar wani jami’in Turkiya.

A yau Laraba kayan agajin da za’a kai gaza sun biya ta tashar ruwan Al-Arish dake kasar Masar, a karon farko tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a ranar 19 ga watan Janairun da muke ciki, kamar yadda wani jami’in Turkiya da majiyoyi a Masar suka bayyana.

Jirgin ruwan mallakin kasar Turkiya, na makare da tan 871 na kayan agajin da suka hada da janaretoci 300 da bandakunan tafi da gidanka 20, da tantuna 10, 460 da kuma barguna 14, 350, a cewar wani jami’in Turkiya.

“A shirye muke mu warkar da raunukan ‘yan uwanmu na Gaza mazansu da mata tare da biyan bukatunsu na matsugunin wucin gadi,” kamar yadda ministan cikin gidan Turkiya Ali Yerlikaya ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba.

Wata tawaga daga kungiyar bada agajin “Red Crescent” ta kasar Masar ce ta karbi kayan agajin na Turkiya kafin ta tsara yadda za’a shigar dasu zirin Gaza, a cewar wata majiya a tashar jiragen ruwan da kuma wasu majiyoyi 2 daga kungiyar bada agajin “Red Crescent” ta kasar Masar kamar yadda kamfanin dillancin labaran Afp ya bayyana.

A makon daya gabata, daruruwan manyan motoci makare da kayan agaji ne suka shiga Gaza bayan fara amfani da yarjejeniyar sulhu, sakamakon shafe fiye da watanni 15 ana gwabza yakin da harin da kungiyar Hamas ta kaiwa Isra’ila na ranar 7 ga watan Oktoban 2023, wanda ba’a taba kai makamancinsa ba ya haddasa.

Izuwa ranar 1 ga watan Disamban daya gabata, an rushe ko lalata kusan kaso 69 cikin 100 na gine-ginen dake yankin Falasdinawa, a cewar Majalisar Dinkin Duniya. An raba kusan ilahirin al’ummar Gaza miliyan 2.4 da muhallansu akalla fiye da sau daya.