Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Lafiyar Lebanon Ta Ce A Kalla Mutane 22 Aka Kashe Baya Ga Wasu 124 Da Aka Ji Ma Rauni


Israel Flag Flags Army Soldier Soldiers - War - HAMAS - Hezbollah - Lebanon - GAZA - Palestinian Hamas - Middle East
Israel Flag Flags Army Soldier Soldiers - War - HAMAS - Hezbollah - Lebanon - GAZA - Palestinian Hamas - Middle East

Sojojin Isira’ila sun bude wuta kan Falasdinawa a yankunan Lebanon da Gaza har su ka kashe mutane 23 baya ga wadanda su ka raunata.

Akwai alamar cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Isira’ila da mayakan Hezbollah a kudancin Lebanon, da kuma Hamas a Gaza, ta shiga wani yanayi mai sarkakkiya zuwa jiya Lahadi, yayin da sojojin Isira’ila su ka bude wuta kan Falasdinawa a yankunan biyu, har su ka kashe mutane 23 baya ga wadanda su ka raunata.

A Lebanon, Ma’aikatar Lafiya ta ce a kalla mutane 22 aka kashe baya ga wasu 124 da aka ji ma raunuka, a daidai lokacin da Isira’ila ke tabbatar da cewa, ba za ta janye sojojinta cikin wa’adin kwanaki 60, kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wutar da ta cimma a watan Nuwamba da Hezbollah ta tanada ba.

Jiya Lahadi dai, fadar Shugaban Amurka ta White House, ta fitar da wata sanarwa mai cewa, jituwar da aka cimma tsakanin Lebanon da Isira’ila, wadda Amurka ke sa ido a kai, za ta ci gaba da aiki har ranar 18 ga watan Fabrairu.

Isra’ila ta zargi mayaka da sojojin Lebanon da gaza cika sharudan yarjejeniyar. Sojojin Isra’ila sun ce sun yi “Harbin gargadi” ta kan wadanda ta ke zargi sannan ta ce ta tsare wasu mutane da bat tantance alkaluman su ba.

A bisa sharudan yarjejeniyyar tsagaita wutar, an bukaci Hezbollah ta janye mayakan ta daga arewacin kan iyakar Isra’ila sannan Isra’ila ta janye dakarun ta daga Lebanon.

Cikin wata sanarwar da ta fitar, Majalisar Dinkin Duniya ta ce dakarun tsaron ta masu tabbatar da zaman Lafiya a Lebanon, da aka fi sani da UNIFIL a takaice, sun yi gargadin cewa, wannan mataki na da mahimmanci don dada kiyaye tabarbarewar yanayin.”

Ta bukaci sojojin Isra’ila su guji harbin fararen hula, sannan su kuma ‘yan Lebanon, su kiyaye umarnin sojojin kasasr su.”Sanarwar ta jaddada cewa, ci gaban rikicin zai raunata yanayin tsaron da aka samu mai rauni.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG