Takwas daga cikin Yahudawan da ake garkuwa dasu daya kamata a saki a gabar farko ta yarjejeniyar sulhu tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas sun mutu, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin Isra’ila David Mencer ya bayyana a yau Litinin.
“An riga an sanar da iyalansu halin da ‘yan uwansu ke ciki,” kamar yadda Mencer ya shaidawa manema labarai, ba tare da fayyace sunayen mamatan ba.
Hakan na nufin daga cikin wadanda ake garkuwa dasu 26, 18 ne kawai ke raye.
Yarjejeniyar sulhun, da aka sanar a farkon watan janairun da muke ciki bayan shafe watanni ana tattaunawa ba tare da nasara ba, ta fara aiki ne a ranar 19 a watan Janairun, inda ta kawo karshen yakin da aka shafe fiye da watanni 15 ana gwabzawa wanda harin da Hamas ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 ya haddasa shi.
A karkashin gabar farko ta yarjejeniyar, za’a saki yahudawa 33 dake hannun mayakan Hamas a Gaza domin musayar fiye da falasdinawa 1, 900 dake rike a hannun Isra’ila.
An saki matan Yahudawa 7 tun bayan fara amfani da yarjejeniyar sulhun, haka kuma an saki Falasdinawa fursunoni 290.
Dandalin Mu Tattauna